Amfanin ‘Ya’Yan Bishiyan Mena Ga Lafiya

AMFANIN ‘YA’YAN NEEM GA LAFIYA:
1. Maganin sanyi da infection: Yana da kashi mai karfi akan kwayoyin cuta (bacteria da fungi), musamman na al’aura.
2. Tace jini: Yana taimaka wa jiki wajen fitar da gubobi da tsaftace jini.
3. Rage zafin ciki da ciwon mafitsara: Ana amfani da shi don rage ciwon ciki mai nasaba da infection da zafi lokacin fitsari.
4. Karfi ga fata da gashi: Ana yin man ‘ya’yan Neem don shafawa a fata da gashi domin kawar da kaikayi, dandruff da kuraje.
5. Maganin Malaria: A wasu yankuna ana amfani da shi wajen rage radadin malaria ko zazzabi.
6. Maganin kuraje da dauda a ciki: Yana fitar da gubar worms daga hanji da kuma tsaftace ciki.
7. Rage yawan sukari a jini: Wasu na amfani da shi wajen taimakawa rage yawan sugar ga masu ciwon suga (diabetes).
8. Maganin ciwon hakori: Ana tauna ‘ya’yan ko amfani da man neem don tsaftace baki da hana kamuwa da cututtuka a hakori da gusi.
9. Karfin garkuwar jiki: Yana ƙarfafa garkuwar jiki domin yaki da cututtuka.
10. Yana taimakawa wajen hana haihuwa (Natural Contraceptive): A gargajiya, mata suna amfani da shi don hana daukar ciki na dan lokaci — amma wannan yana bukatar kulawa sosai.
LURA: Kada a sha da yawa ba tare da shawarar masani ba, musamman ga mata masu ciki ko masu fama da ciwon hanta.